Ina son in zama kocin Faransa - Zidane

zidane
Image caption Zinedine Zidane

Darektan Wasanni na kulob din Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana cewar yana sha'awar zamowa kocin tawagar 'yan kwallon Faransa a nan gaba.

A shekara ta 2006 ne Zidane yayi ritaya daga buga kwallo amma kuma a watan Yunin 2009 aka nadashi a matsayin mai baiwa shugaban Real Madrid Florentino Perez shawara.

A farkon wannan shekarar ne aka nada Zidane a matsayin Darektan wasanni na Real, amma kuma a yanzu bisa dukkan alamu tsohon dan kwallon Faransan nada sha'awar kasancewa mai horadda 'yan kwallo.

A halin yanzu dai Laurent Blanc ne kocin Faransa wanda ya maye gurbin Raymond Domenech bayan gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010 a Afrika ta Kudu.