An damke mahaifin Rooney akan cogen wasa

rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wayne Rooney Sr da Steve Jennings

Mahaifin dan kwallon Manchester United Wayne Rooney na daga cikin mutane tara da aka damke bisa zargin coge a lokacin yin cacan sakamakon wasan kwallon kafa.

Wayne Rooney Sr da wasu mutane bakwai suna tsare ne a Merseyside. Sannan kuma an tsare dan kwallon kulob din Motherwell FC Steve Jennings a gidansa dake Glasgow.

'Yan sanda sun ce an tsare mutannen ne bisa hada baki wajen yin zamba.

Binciken nada nasaba da wasa tsakanin kulob din Motherwell da Hearts.

A lokacin wasan dai Jennings wanda aka riga aka baiwa katin gargadi, daga bisani an kore shi gabda a tashi wasan inda aka doke Motherwell a gidanta daci biyu da daya.