EFCC ta bayar da sammacin kame Danjuma Goje

Danjuma Goje Hakkin mallakar hoto goggle
Image caption Danjuma Goje ya mulki jihar Gombe tsawon shekaru takwas

Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta bayar da sammacin kame tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje.

"Muna bincike kan zargin da ake masa na almubazzaranci da kuma salwantar da dukiyar jama'a da yawanta ya kai naira biliyan 52," a cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC Femi Babafemi.

"Mun neme shi, mun aika masa da takardar gayyata, amma ya ki zuwa," kamar yadda Babafemi ya shaida wa BBC.

"Tun lokacin da muka aika masa da takardar sammaci ya shiga wasan buya da mu, abinda ya sa muka bayyana sammacin kama shi ruwa a jallo."

Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan ne wanda ya mulki jihar ta Gombe daga shekara ta 2003 zuwa 2011 - wanda kuma a yanzu dan majalisar dattawa ne, bayan da ta samu korafi daga wasu 'yan jihar kan yadda ya gudanar da mulkin na sa.

Hukumar ta EFCC ta nemi hukumomin tsaro na kasar da ma jama'ar gari da su taimaka mata wajen kame tsohon gwamna Goje.

A ranar Alhamis ma EFCC ta kame tsaffin gwamnonin kasar uku da suka hada da na Oyo Alao Akala da Ogun Gbenga Daniel da na Nassarawa Aliyu Akwe Doma.

Suma dai ana zarginsu kan wasu lamura da suka aikata da ake ganin sun sabawa doka a lokacin da suka jagoranci jihohin na su.

Hukumar ta EFCC ta dade tana takun saka da tsaffin gwamnoni a Najeriyar da ma wasu 'yan siyasa da dama.