A shirye Rooney yake ya taka leda - Capello

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mahaifin Wayne Rooney wanda ake zargi da yunkurin coge

Kocin Ingila Fabio Capello ya ce Wayne Rooney ya shaida masa cewa a shirye yake ya taka leda a wasansu da Montenegro duk da kamen da akaiwa mahaifinsa.

Mahaifin Wayne Rooney na daya daga cikin mutane taran da aka kama ranar Alhamis a wani bincike kan zargin coge a wasa.

Amma Capello ya ce dan wasan "ba shi da wata damuwa" kan lamarin a daidai lokacin da ake shirin wasan na share fagen shiga gasar cin kofin Turai na 2012.

"Ya shaida min cewa ba wata matsala'," a cewar kocin na Ingila. "Ya tabbatar da cewa wannan ba wata matsala ba ce."

Kyaftin din Ingila John Terry ya kara da cewa: "Hankalin Wayne ya na kan wasan. Dukkanmu mun fahimci muhimmancin haka. Ya na da muhimmanci a gare shi ya taka leda. Wannan shi ne kawai abinda ya dame mu."