Capello na neman magajin Rooney

Rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan kyatar ce ta sa aka baiwa Rooney jan kati

Kocin Ingila Fabio Capello na neman wanda zai maye gurbin Rooney, saboda ba za a fara gasar cin kofin Turai ta 2012 da dan wasan ba saboda jan katin da ya samu.

A ranar Juma'a ne aka baiwa Rooney jan kati a wasansu da Montenegro, abinda ya sa kuma ba za a fara gasar da shi ba.

Dan wasan mai shekaru 25, ba zai buga wasan farko na gasar ba wacce za a gudanar a kasashen Poland da Ukraine bayan da ya taka Miodrag Dzudovic a wasan share fagen da suka tashi 2-2 a Podgorica.

Akwai yiwuwar hukuncin ya zarta na wasa daya, bayan Uefa ta saurari rahoton alkalin wasa Wolfgang Stark.

Shirye-shiryen na Capello sun fuskanci koma baya, kuma a yanzu ya na tunanin ajiye Rooney a wasannin sada zumuntar da kasar za ta buga domin shiryawa gasar ta 2012.

A yanzu ta tabbata cewa Rooney ba zai taka leda a wasan da Ingila za ta kara da Spain a filin wasa na Wembley ba.

"Rooney ba zai buga wasan Spain ba. Ina so na gwada sabbin 'yan wasa da ma sabon tsarin taka leda," a cewar Capello.