Zambia ta kori kocin 'yan kwallonta Bonetti

Dario Bonetti
Image caption Dario Bonetti

Zambia ta sallami kocin 'yan kwallonta Dario Bonetti duk da taimakawa kasar tsallakewa zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a karshen wannan makon.

Hukumar kwallon Zambia-FAZ ta ce kocin da kashin kansa ya tafi, a yayinda Bonetti ya karyata inda yace bada son ransa zai tafi ba.

Bonetti yace"ra'ayina shine in cigaba da zama tunda nayi aiki na, na tsallakar da kasar zuwa gasar Afrika".

A watan Yulin 2010 ne aka nada Bonetti a kwangilar shekaru biyu, kuma ya ce ya kamata a sabunta masa kwangilar tunda ya samu gurbin zuwa gasar cin kofin 2012.

Bonetti ya ce zai kira taron manema labarai don ya fasa kwai.