Euro 2012: An ware Ireland da Portugal

Richard Dunne na Ireland
Image caption Richard Dunne ne ya zira kwallon da ta baiwa Ireland dama

Jamhuriyar Ireland na daya daga cikin kasashe hudun da aka ware a jerin kasashen da za su shiga wasan kifa-daya-kwala domin zuwa gasar cin kofin kwallon Turai ta 2012.

Hakan na nufin za su kara da daya daga cikin Turkiyya ko Bosnia-Hercegovina ko Estonia ko kuma Montenegro a wasanni biyun da za a kara domin shiga gasar ta badi.

Portugal da Croatia da Jamhuriyar Czech su ne sauran kasashen da hukumar kwallon Turai Uefa ta ware, saboda karfin tawagarsu.

Jamhuriyar Ireland ta doke Armenia da ci 2-1 ranar Talata abinda ya bata damar tsallakewa zuwa wasan kifa-daya-kwalan.

Za a raba kasashen ne ranar Alhamis a birnin Krakow kafin gasar da za a gudanar a kasashen Poland da Ukraine.

Za a fafata zagayen farko na wasannin a ranakun 11 da 12 na watan Nuwamba, da kuma zagaye na biyu a ranar 15 ga watan na Nuwamba.