Damuwa kan raba kudaden shigar Premier

Damuwa kan raba kudaden shigar Premier
Image caption Yarjejeniyar haska gasar Premier za ta kare a 2013

Liverpool ta kalubalanci yadda ake sayar damar kallon gasar Premier ta Ingila ga sauran kasashen duniya - da ma yadda ake raba kudaden.

Manajan daraktan Liverpool ya ce kamata ya yi Liverpool da sauran manyan kulob-kulob su samu kaso mai tsoka daga kudaden da ake sayar da gasar a waje, saboda sun fi yawan magoya baya.

Ian Ayre na tsoron sauran kungiyoyin Turai za su yi wa na Ingila tazara idan aka ci gaba da raba kudaden shigar da ake samu daga kasashen waje daidai-da-daidai tsakanin kungiyoyi 20 na gasar ta Premier.

Ayre ya ce: "Sauran kungiyoyin Turai da ba sa bin wannan tsari. Suna samun kudaden shiga masu yawa domin sayen manyan 'yan wasa."

Yarjejeniyar haska gasar Premier ta Ingila wacce ta kai fan biliyan daya da miliyan dari hudu, za ta kare ne a shekara ta 2013.

A karkashin dokar da ake amfani da ita yanzu, wajibi ne kulob 14 su amince kafin a samu wani sauyi.

Sai dai Ayre na ganin Liverpool tare da Manchester United da Chelsea da kuma Arsenal - sun cancanci samun kaso mai tsoka.