NFF bata yanke shawara ba akan Siasia

siasia
Image caption Samson Siasia

Sai a mako mai zuwa ne hukumar dake kula da kwallon kafa a Najeriya zata yanke hukunci akan makomar kocin Super Eagles Samson Siasia.

A ranar Alhamis ne kwamitin kwararru na NFF ya tattauna batun kocin, amma ya ce ya mikawa kwamitin zartarwa shawararsa.

Siasia na fuskantar matsin lamba tun lokacin da Super Eagles ta kasa samun gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.

Majiyoyin BBC sun nuna cewar akwai rarrabuwar kawuna a hukumar NFF din akan batun barin Siasia ko kuma korarsa.