Uefa ta raina wa Ingila hankali - Moyes

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahotanni sun ce Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA za ta daukaka kara

Kocin Everton David Moyes ya ce dakatarwar da Uefa ta yi wa Wayne Rooney na wasa uku a gasar cin kofin Euro 2012 "rainin hankali ne".

Kocin ya yi amannar cewa Uefa ta so yin la'akari da halayyar dan wasan ne, amma hukuncin "ya wuce gona-da-iri".

Shi ma kocin Tottenham Harry Redknapp ya bayyana tsawon dakatarwar da cewa ta ba shi "mamaki kuma koma baya ne".

Moyes, wanda ya koyar da Rooney daga 2002-2004, ya ce: "Ina ganin dakatarwar wasa uku rainin hankali ne. Bai dace ba, kuma ina ganin ya yi yawa."

Kocin na Everton na ganin Rooney, dan shekaru 25, ya kamata ya shiga cikin tawagar koci Fabio Capello ta gasar cin kofin Euro da za a yi a kasashen Poland da Ukraine.

A ranar Alhamis ne Uefa ta dakatar da Rooney tsawon wasanni uku sakamakon jan katin da aka bashi a wasan share fagen shiga gasar cin kofin Euro na 2012.

Hakan dai na nufin ba zai buga wasanni ukun farko da Ingila za ta fafata a gasar ba.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA za ta daukaka kara kan hukuncin.

Karin bayani