PSG na zawarcin David Beckham

David Beckham Hakkin mallakar hoto ap
Image caption A watan Disamba ne kwantiragin Beckham za ta kare

Paris Saint-Germain ta yi yunkuri na farko domin sayen tsohon kyaftin din Ingila David Beckham idan kwantiraginsa ta kare da LA Galaxy a watan Disamba.

PSG ta tattauna ta wayar tarho da wakilan dan wasan amma har yanzu ba a yi wata ganawa a hukumance ba.

Kulob-kulob da dama da suka hada da na Ingila sun nuna sha'awarsu a kan Beckham, wanda aka fahimci cewa ya na son koma wa wani League mai kwari.

Sai dai bai fitar da ran ci gaba da zama a LA ba, inda iyalinsa suka riga suka saba.

Tsohon dan wasan na Real Madrid da Manchester United, wanda kwantiraginsa za ta kare a ranar 31 ga watan Disamba, zai bayyana inda zai koma a watan Nuwamba da zarar an kammala gasar League ta Amurka.

Galaxy ne ke jagoranci da tazara mai yawa a rukuninsu, kuma sun samu gurbi a zagayen kifa-daya-kwalan da za a yi.