Beckham zai ci tudu biyu idan ya koma PSG

beckham Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David Beckham

Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Paris Saint-Germain zata tsohon kyaftin din Ingila David Beckhman damar ya kasance dan kwallonta sannan kuma a dinga sharhi akan kwallon kafa a Talabijin.

Rahotanni na nuna cewar Beckham zai taka leda sannan kuma yayi aiki da Al-Jazeera Sport.

Mai kungiyar PSG Nasser Al-Khelaifi na saran sayen dan wasan mai shekaru 36 bayan kwangilarsa ta kare a wata mai a kungiyar LA Galaxy.

Khelaifi wanda shine shugaban gidan talabijin na Aljazeera yana son yin amfani da Beckham don ya habbaka gidan talabijin din.