Zan bi hakki na akan Suarez-Evra

suarez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lius Suarez

Dan kwallon Manchester United Patrice Evra ya shaidawa kocinsa Sir Alex Ferguson cewar yanason yabi hakkinsa akan zargin da ya yiwa dan wasan Liverpool Luis Suarez akan cewar yayi masa kalamai na wariyar launin fata.

Evra yayi zargin ne bayan wasan da Manchester United ta tashi kunen doki tsakaninta da Liverpool a ranar Asabar.

Dan wasan Faransa ya ce sake duba hoton bidiyon wasan zai nuna tabbacin cewar Suarez ya zage shi, a yayinda Suarez din yace yaji mamakin wannan zargin.

Ferguson yace"Nayi magana da Patrice, ya tsaya kaida fata cewar zai bi kadin lamarin".

Fifa da Uefa suna da hukunci mai tsauri akan batun batanci na wariyar launin fata a kwallon kafa.