Ina son in dade a Manchester City-Mancini

manicni Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya bayyana cewar yanason ya kasance tare da kulob din na karin wasu shekaru uku zuwa hudu masu zuwa.

Dan Italiyan wanda kwangilarsa za ta kare a shekara ta 2013, ya jagoranci City ta lashe kofin FA a kakar wasan data wuce kuma shine babban kofin farko cikin shekaru 35.

Kuma a yayinda kulob din ke jagoranci a saman teburin gasar, Mancini ya ce"Zan so in tsaya a nan, ina tunanin cewar Manchester City na daga cikin manyan kulob a duniya".

Amma dai ya kara da cewar basu soma tattauna sabuwar kwangila ba.

Mancini mai shekaru 46 ya maye gurbin Mark Hughes ne a matsayin kocin City a watan Disambar 2009.