Blatter zai sa a wallafa takardun badakalar kudi

blatter
Image caption Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Sepp Blatter yana shirin daukar wani mataki mai karfi nayin kira a bada takardun kotun dake nuna cewar manyan jami'an Fifa sun karbi cin hanci.

A baya dai Fifa ta yita kare manema labarai daga samun takardun.

BBC ta fahimci cewar Blatter zai matsa a wallafa takardun a taron kwanaki biyu na Fifa da za ayi a Zurich daga ranar Alhamis.

Takardun na kunshe ne da bayanan dake nuna cewar akwai badakalar da aka yi wajen bada talla na Fifa da kuma batun bada hakkin mallakar watsa kwallon kafa a duniya a shekarar 1990.

A bara, lauyoyin Fifa sun bada dala miliyon biyar da rabi wajen boye sunayen masu laifin.