Cin Hanci:Diakite zai daukaka kara akan FIFA

fifa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shalkwatar FIFA

Jami'in kwallon a kasar Mali Amadou Diakite a ranar Laraba zai daukaka karar dakatarwar shekaru biyu da Fifa tayi masa daga shiga harkokin kwallon kafa a duniya.

An dakatar da Diakite ne a watan Nuwamban bara akan batun badakalar daya faru lokacin zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da kuma 2022.

Dakatarwar ta Fifa ta biyo bayan binciken da akayi ne akan cewar sun karbi toshiyar baki don bada kuri'a.

A wannan lokacinne kuma aka dakatar da dan Najeriya Amos Adamu dama wasu jami'an Fifa bisa zargin cin hanci.

Jaridar Sunday Times zargin cewar Diakite ya bayyanna cewar za a baiwa jami'an Fifa 'yan Afrika dala miliyon daya ko kuma fiye don sa sayarda kuri'arsu.