2012:Sukar da akayi min ta wuce kima-Osaze

oasze
Image caption Osaze Odemwingie

Dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie ya bayyana cewar yayi matukar damuwa bisa sukarsa da aka yita yi akan kasawar Najeriya wajen samun gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a badi.

Magoya baya da dama sun zargeshi akan barar da dama inda aka tashi biyu da biyu tsakaninsu da Guinea a yayinda Najeriya ke bukatar nasara a wasan.

Yace"Masu suka na nemar hujja ne amma ina ganin cewar an kururuta batun".

Osaze ya kara da cewar"Ina ganin abin ya shafi kowa ne, amma sukar da aka yita min nada nasaba da rashin jituwa ta da koci".

A watan Maris ne Samson Siasia ya ajiye Odemwingie saboda ficewa daga sansani ba tare da izini ba.