Na amince da jan katin Vidic - Ferguson

Ferguson da Vidic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne wasan Vidic na farko bayan jinyar da ya yi

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce ya fahimci dalilin da ya sanya alkalin wasa ya kori Nemanja Vidic a wasan da United ta doke Otelul Galati da ci 2-0.

Alkalin wasa Felix Brych na kasar Jamus ya baiwa Vidic jan kati ne kai tsaye bayan da ya tade Gabriel Giurgiu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Ferguson ya ce: "Na fahimci matakin da alkalin wasan ya dauka.

"Ba mamaki akwai banbanci a Jamus, amma dai abin ya dan yi tsauri. Kamata ya yi ace katin gargadi aka bashi.

Vidic, wanda ya dawo a karon farko bayan ya yi fama da jinya zai fuskanci dakatarwar wasa daya.

Sai dai kamar yadda ta faru da Wayne Rooney a gasar share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Turai, Uefa za ta iya dakatar da shi wasa biyu ko uku.

Ferguson ya kara da cewa: "Na sake kallon lamarin, kuma hakika kafarsa ta yi sama da yawa."