Kocin Equitorial Guinea ya yi murabus

henri
Image caption Henri Michel

Kocin Equitorial Guinea Henri Michel ya yi murabus daga mukaminsa.

Babu dalili kawo yanzu da aka bada akan abinda ya sanya shi barin mukamin, ganin cewar Equitorial Guinea ce zata dauki bakuncin gasar cin kofin Afrika tare da Gabon.

A ranar Litinin ne Henri Michel tare da mataimakinsa suka tattauna da shugaban kwallon kasar Bonifacio Manga Obiang.

Michel ya soma aiki da Equitorial Guinea ne a watan Junairu kuma kwangilarsa zata kare ne a watan Fabarairun badi lokacin da aka kamalla gasar cin kofin Afrika.

Hukumar kwallon kasar Equitorial Guinea (feguifoot) nada sauran wattanni uku don samun wani sabon kocin da zai jagoranci tawagar 'yan kwallon kasar zuwa gasar ta Afrika.