FIFA:Ivory Coast ce ta farko,Najeriya ta shida

drogba Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Didier Drogba,kyaftin din Ivory Coast

Har yanzu Ivory Coast ce ta farko a fagen kwallon kafa a nahiyar Afrika, kamar yadda hukumar kwallon ta duniya Fifa ta fitar da jerin karfin kasashe.

Ba'a samu sauyi ba a jerin kasashe ukun farko kamar yadda yake a watan daya wuce saboda Masar ce ta biyu sannan Ghana ce ta uku.

Masar din ta cigaba da rike matakinne saboda nasararta akan Nijer daci uku da nema a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika.

A yayinda ita kuma Black Stars ta haskaka wajen doke Sudan daci biyu da nema, amma Ghanar ce ta talatin da uku a duniya.

Najeriya ce ta shida a Afrika amma ta 44 a duniya.

Manyan kasashen Afrika goma:

1. Ivory Coast (19 a duniya)

2. Masar (29 a duniya)

3. Ghana (33 a duniya)

4. Algeria(35 a duniya)

5. Senegal (42 a duniya)

6. Nigeria (44 a duniya)

7. Kamaru (47 a duniya)

8. Afrika ta Kudu (49 a duniya)

9. Burkina Faso (54 a duniya)

10. Morocco (56 a duniya)