Dole ne kulob su dinga nitsewa -Redknapp

redknapp
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce idan aka cire tsarin nitsewa da hayewa sama a Premier gasar zata zama babu armashi kwata kwata.

Redknapp ya kuma ce karfin fada aji na masu mallakar kulob daga kasashen waje, zai iya sa a koma buga wasu wasanni gasar a kasashen ketare.

Yace"Ta yaya za ace babu dagowa sama ko kuma nitsewa".

Ya kara da cewar" ba zai yiwu samu masu kulob 'yan kasashen waje su zo su canza mana wasa ba".

A farkon wannan makonne, shugaban kungiyar masu horadda 'yan kwallon Richard Bevan yace wasu 'yan kasashen wajen wadanda suka mallaki kulob a Ingila suna son a canza tsarin gasar.