Afrika ta Kudu ta janye kokenta akan Nijer

safa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar SAFA a Afrika ta Kudu

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika ta Kudu wato SAFA ta janye takardar koken data aikewa CAF akan yadda tsarin da ake bi wajen tsallakewa zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika.

SAFA ta kuma nemi afuwa saboda mummunar rawar da Bafana Bafana ta taka wajen neman gurbin zuwa gasar.

Sannan kuma hukumar ta SAFA ta taya Nijer murnar samun wannan gurbin na zuwa gasar.

Afrika ta Kudu ta gaggauta mika takardar koke ne a wajen CAF lokacin da aka bayyana cewar Nijer ce ta fito daga rukunin.

Nijer ta tsallake ne duk da cewar makinta dai dai ne dana Afrika ta Kudu da Saliyo.