Blatter ya ce za a saki takardun bincike

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blatter na fuskantar matsin lamba kan wannan binciken

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter, ya ce zai saki takardun da za su bayyana sunayen jami'an da ke da hannu a badakalar cin hanci.

Batun dai ya shafi wata badakala ce kan yarjejeniyar talla tsakanin wani kamfani da kuma Hukumar ta FIFA.

FIFA na ta kokarin ganin ta hana wata kotun kasar Switzerland fitar da takardun wadanda za su bayyana jami'an da suka karbi kudi daga tsohuwar cibiyar tallata harkokin kasuwanci na ISL, wacce ta rushe a shekara ta 2001.

Blatter ya fada a ranar Juma'a cewa kwamitin zartarwa na FIFA zai tattauna kan takardun a taron da za ta yi a watan Disamba a kasar Japan.

Ya kuma kara da cewa wani kwamiti na musamman mai zaman kansa zai bayar da shawara kan yadda za a ci gaba da batun.

Blatter ya bayyana cewa za a sake bude takardun na ISL a daidai lokacin da yake bayyana aniyarsa ta kawo sauyi a hukumar - wacce batun cin hanci da rashawa ya kankane.

"FIFA a matsayinta na hukuma babu cin hanci a cikinta," a cewar Balatter.