Rugby:New Zealand ta lashe gasar duniya

new Hakkin mallakar hoto ALL SPORT Getty
Image caption Tawagar All Black ta New Zealand

New Zealand ta zama zakara a gasar zari ka ruga ta duniya wato Rugby a karon farko cikin shekaru ashirin da hudu bayan ta doke Faransa a wasan karshe daci takwas da bakwai.

Faransa ta haskaka sosai a gasar amma kuma a wasan karshen mai masaukin baki wato New Zealand ta kwace garin.

A dai dai lokacin da aka hura tashi, sai filin wasan ta dauke da shewa da kade-kade na murnar wannan nasarar da tawagar All Blacks tayi a karon farko tun shekarar 1987.

Zakarun gasar rugby a duniya:

* 1987: New Zealand ta doke Faransa 29-9 * 1991: Australia ta doke Ingila 12-6 * 1995: Afrika ta Kudu ta doke New Zealand 15-12 * 1999: Australia ta doke Faransa 35-12 * 2003: Ingila ta doke Australia 20-17 * 2007: Afrika ta Kudu ta doke Ingila 15-6 * 2011: New Zealand ta doke Faransa 8-7