Amoebi zai jinyar makwanni shida a Newcastle

ameobi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shola Ameobi

Kocin Newcastle United Alan Pardew ya bayyana cewar dan kwallonsa Shola Ameobi zai yi jinyar makwanni hudu zuwa shida.

Ameobi mai shekaru 30 ya buga wasanni bakwai a kakar wasanni ta bana a Newcastle.

Pardew yace"zamu yi kewarsa damu da magoya bayanmu".

Tsohon dan wasan Ingila a matakin 'yan kasada shekaru 21, baya samun damar bugawa saboda Demba Ba da kuma Leon Best.

Ameobi ya koma Newcastle ne tun yana shekaru 13 inda ya buga wasanni 210 tare da zira kwallaye 71.