FA na nazari akan sukar da Villas-Boas yayi

villas boas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andre Villas-Boas

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila wato FA ta soma nazari akan sukar da kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya yiwa alkalin wasa Chris Foy bayan Chelsea ta sha kashi a wajen QPR daci daya me ban haushi.

Villas-Boas ya ce Foy ya nuna "abu mare kyau" daya canza sakamako a wasan.

Hukumar ta FA na sane da kalaman kocin dan kasar Portugal kuma a ranar Laraba zata yanke shawara ko zata tuhumi kocin bisa saba ka'ida.

Villas-Boas zai iya fuskantar tara ko kuma dakatar dashi idan aka kamashi da laifi.

Foy ya baiwa QPR fenariti sannan kuma ya kori Jose Bosingwa da Didier Drogba kafin a tafi hutun rabin lokaci.