An kori kocin Indomitable Lions na Kamaru

clemente
Image caption Javier Clemente

Kamaru ta kori kocin Indomitable Lions Javier Clemente duk da cewar akwai sauran watanni takwas kafin kwangilarsa ta kare.

A ranar Talata ne hukumar Fecafoot ta tabbatar da sallamarsa, abinda ya kawo karshen rashin tabbas akan makomar dan Spaniya din.

Clemente ne ya jagoranci mummunar rawar da Kamaru ta taka na kasa samun zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a badi.

Sakatare Janar na hukumar kwallon Kamaru Sidiki Tombi ya ce "Mun bayyanawa Clemente da mataimakinsa cewar an sallamesu daga aiki".

Ana saran kocin kungiyar Coton Sports Denis Lavagne shine zai maye gurbin Clemente.

Tombi ya kara da cewar" Za a nada sabon koci nan bada jimawa ba".

An nada Clemente a watan Agustan bara inda ya maye gurbin Paul Le Guen bayan da aka fidda Kamaru a gasar cin kofin kwallon duniya a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.