Henri Michel ya koma Equatorial Guinea

Henri Michel
Image caption Michel ya koma Equatorial Guinea bayan ya bari a makon da ya gabata

Henri Michel ya koma Equatorial Guinea a matsayin koci mako guda bayan da ya yi murabus daga kasar wacce za ta karbi bakuncin hadin gwiwa na gasar cin kofin kasashen Afrika badi.

Kocin dan kasar Faransa ya koma ne bayan da aka kori shugaban hukumar wasanni ta kasar Ruslan Obiang.

Michel ya samu sabani ne da shugabannin hukumar wasannin kasar kan yadda ya ke zabar 'yan wasan tawagar kwallon kasar, abinda ya sanya shi yin murabus.

A yanzu kocin ya koma kasar a daidai lokacin da ake shirin rarraba kungiyoyin da za su taka leda a gasar ta 2012 ranar Asabar.

Wakilin BBC Matthew Kenyon, wanda yanzu haka yake birnin Malabo, ya ce dan Najeriya Stephen Keshi na daga cikin wadanda aka ware domin maye gurbin Michel kafin a kori Obiang, wanda dan shugaban kasar ne.

Babu shakka dawowar Michel za ta karawa tawagar kasar karfin gwiwa makonni biyu kafin su karbi bakuncin Madagascar a wasan share fage na shiga gasar cin kofin duniya ta 2014.

Kocin ya fara aiki da tawagar ne a watan Janairu, kuma kwantiraginsa za ta kare ne bayan kammala gasar cin kofin kasashen Afrika, wanda za a kammala a watan Fabreru.