An nada Lavagne a matsayin kocin Kamaru

etoo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o

An nada Denis Lavagne a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallon Kamaru inda ya maye gurbin dan kasar Spain Javier Clemente.

Lavagne ya bar mukaminsa na kocin Coton Sport kuma zai fara aiki ne take da tawagar Indomitable Lions.

An kori Clemente ne bayan da Kamaru ta kasa samun gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za ayi a Gabon da Equatorial Guinea.

A watan Yuni ne Kamaru zata fara buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya da za ayi a Brazil a 2014.

Indomitable Lions na rukuni guda da Libya da kuma kasashen da suka zasu samu nasara a karawa tsakanin Swaziland da DR Congo da kuma na Guinea Bissau da Togo.

Martin Ndtougou Mbile shine zai kasance mataimakin Lavagne a yayinda Pierre Mbarga zai zama kocin masu tsaron gida.

Kamaru ta lashe gasar kofin Afrika sau hudu, kuma kasa samun gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika a badi ba karamin cikas bane ga kasar.