Tavez zai kai karar Mancini gaban kotu

Mancini Hakkin mallakar hoto elvis
Image caption A lokacin da mutanen biyu na dasawa - Roberto Mancini da Carlos Tevez

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa mai yiwuwa Carlos Tevez ya kai karar kocin Manchester City Roberto Mancini, bisa zargin bata masa suna.

A ranar Talata ne City ta ci tarar Tevez albashin mako hudu - kusan dala miliyan daya - kan abinda suka ce sabawa ka'idojin kwantiraginsa a wasan su da Bayern Munich.

Wani bincike da kulob din ya yi ya samu Tevez da kin amince wa ya tashi ya motsa jiki a wasan.

Sai dai an shawarci Tevez cewa kalaman da Mancini ya yi bayan wasan, za su iya kasance wa na bata masa suna.

Dan wasan na da kwanaki 14 domin ya daukaka kara ga hukumomin kulob din.

Shi dai ya dage kan cewar babu wanda ya gaya masa cewa za'a sa shi a wasan, don haka yana tunanin shigar da kara a gaban kotun sauraran koke-koke ta gasar Premier.

Idan dai bai yi nasara a daukaka karar da zai yi ba, to yana da damar tafiya kotun ta Premier.

Karin bayani