Afrika ta Kudu zata fafata da Ivory Coast

africa ta kudu
Image caption 'Yan wasan Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu zata buga wasan sada zumunci tsakaninta da Ivory Coast a ranar 12 ga watan Nuwamba a wasan kalubale na Nelson Mandela da ake bugawa duk shekara.

Za a buga wasanne a filin wasa na Nelson Mandela Bay dake birnin Port Elizabeth.

Shugaban hukumar kwallon Afrika ta Kudu SAFA Robin Petersen ya ce "Bafana Bafana zata kara da tawaga mai karfi ta Ivory Coast".

Ivory Coast zata zo da manyan 'yan wasa kamarsu Didier Drogba da Salomon Kalou da Yaya Toure da Kolo Toure da kuma Gervinho na Arsenal.

Mataimakin shugaban SAFA Mwelo Nonkonyana ya ce yana saran wasan zai sharewa 'yan Afrika ta Kudu hawayen kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika da za ayi a badi.