An dakatar da Boateng na wasanni biyu

Kevin Prince Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin Prince Boateng

An dakatar da dan kwallon Ghana wanda ke taka leda a AC Milan Kevin Prince Boateng na wasanni biyu a Italiya saboda zagin mataimakin alkalin wasa.

Sannan kuma aka ci tarar kocinsa Massimilliano Allegri Euro dubu biyar.

An kori Boateng ne a wasan da Milan ta casa Roma daci uku da biyu a ranar Asabar saboda zagin mataimakin alkalin wasa, amma kuma a lokacin an riga a canza daga wasan.

Shi kuma Allegri laifinsa shine ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin da aka yankewa dan wasansa.

Sakamakon dakatarwar da aka yiwa Boateng ba zai buga wasansu da Catania da kuma Fiorentina.