Dan Senegal Diouf ya koma Doncaster Rovers

diouf Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption El-Hadji Diouf

Dan kwallon Senegal El-Hadji Diouf ya koma kungiyar Doncaster Rovers a kwangilar watanni uku.

Dan wasan mai shekaru talatin wanda Blackburn ta sallameshi ya koma kulob din dake taka leda a gasar Championship na Ingila ne bayan tattaunawarsa da kocin kulob din Dean Saunders.

Tsohon gwarzon dan kwallon Afrika din a karo biyu,Diuof ya taba taka leda a Liverpool, Bolton, Sunderland da kuma Rangers.

Diouf ya bugawa kasarsa wasannin 69 inda ya zira kwallaye 21.

Zuwan Diouf zai taimakawa Doncaster Rovers saboda kulob din na fama da karancin 'yan wasan gaba.