Redknapp ya jinjinawa Scott Parker

Scott Parker da Redknapp Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Scott Parker yana taka leda sosai a 'yan kwanakin nan

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce rawar da Scott Parker ya taka a wasansu da Queens Park Rangers ta tuna masa shahararren tsohon dan wasan Spurs Dave Mackay.

Gareth Bale ne ya zira kwallaye biyun da suka taimaka wa Spurs ta yi nasara da ci 3-1, sai dai Redknapp ya jinjina wa rawar da Parker, mai shekaru 31 ya taka ne.

"Parker ya bani mamaki, na dade banga ledar da ta kayatar da ni kamar wannan ba," a cewarsa.

"Ba za ka iya hada wani da Dave Mackay ba, wanda na daya daga cikin kwararrun 'yan wasa a nan."

Redknapp ya kara da cewa: "Shi kansa Dave zai yi alfahari da wannan rawar da Parker ya taka. Duk inda kwallo take za ka ganshi. Ya yi tasiri a wasan yadda ya kamata."

Tsohon dan wasan na Spurs Mackay, mai shekaru 76, ya shafe shekaru tara a kulob din, kuma yana cikin tawagar kulob din da suka lashe gasar league da ta FA a shekarar 1961.