Solskajaer ya jagoranci Molde lashe kofi

 Ole Gunnar Solskjaer Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ole Gunnar Solskjaer

Tsohon dan kwallon Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya jagoranci kungiyar Molde ta Norway lashe gasa a karon farko a tarihinta kuma a kakar wasa na farko a matsayin koci.

Dan shekaru talatin da takwas, Solskjaer ya hade da kulob dinne a watan Nuwambar bara, bayan lokacin da ya shafe a matsayin karamin koci a Old Trafford.

Kungiyar Molde ta kasance ta goma sha daya a kakar wasan data wuce amma a yanzu ta lashe kofin gasar duk da cewar akwai sauran wasanni biyu a kamalla gasar.

Molde ta lashe gasar ce bayan ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Stromsgodset a ranar Lahadi.

Solskjaer yace "kulob din ya shafe shekaru dari daya yana jiran wannan lokacin, kuma mun dace da lashe gasar".

Solskjaer ya bar Molde a matsayin dan wasa a shekarar 1996 akan kwangilar fan miliyon daya da rabi.

Kuma dan kasar Norway din ya zira kwallaye 126 a wasanni 366 tare da Red Devils sannan kuma ya lashe kofin gasar zakarun Turai daya dana premier shida da kuma na FA biyu.