Beckham na saran za a kara kiransa a Ingila

beckham Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David Beckham

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ya ce bai fidda ran cewa za a kara kiransa ya bugawa kasarsa kwallo.

Beckham wanda ya buga Ingila wasanni 115, a yanzu shekarun 36 ne abinda yasa wasu ke ganin cewar lokacinsa ya wuce saboda shekaru biyu kenan cifa rabon daya saka rigar kwallon Ingila.

Tsohon dan kwallon Manchester United din ya ce ba zai yi ritaya ba idan kwangilarsa ta kare a karshen Nuwamba tare da kungiyar LA Galaxy.

Yace"Ina cikin koshin lafiya kuma duk dan kwallon daya ji rauni a Ingila a shirye nake in maye gurbinsa".

Beckham ya kara da cewar"Zan so in kara bugawa Ingila kuma nayi ammana hakan zai yiwu".