An nada Keshi a matsayin kocin Super Eagles

keshi
Image caption Stephen Keshi

Najeriya ta nada tsohon kyaftin din kasar Stephen Keshi a matsayin kocin Super Eagles.

Keshi ya maye gurbin Samson Siasia wanda aka kora a ranar Juma'ar data gabata saboda kasa tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za ayi a 2012.

Dan shekaru 49, Keshi ne ya sanya kambum kyaftin din Najeriya lokacin da kasar ta lashe gasar kwallon Afrika a shekarar 1994, sannan kuma a baya ya jagoranci 'yan kwallon Mali dana Togo.

Mataimakin shugaban NFF Mike Umeh ya ce "da gaggarumar rinjaye mu a NFF muka amince da nadi Stephen Keshi a matsayin sabon kocin Super eagles".

Kwangilarsa zata kai har zuwa shekara ta 2014, sannan kuma ana saran Keshi ya tsallakar da Najeriya zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a 2013 da kuma gasar cin kofin duniya a 2014.

An baiwa Keshi damar zaman mataimakansa.