Messi ya kafa tarihin kwallaye 200 a Barca

messi Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Lionel Messi yana murza leda

Lionel Messi ya kasance dan kwallo na biyu a tarihin Barcelona daya zira kwallaye 200 sakamakon kwallaye ukun daya ci a wasan da Barca ta casa Viktoria Plzen daci hudu da nema.

Wannan nasarar ce ta sanya Barcelona ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

Dan Argentina din shine ya bude fagen zira kwallo a minti na 24 kafin ya kara kwallo daya kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Cesc Fabregas ne yaci kwallo ta uku sannan Messi yaci ta hudu.

Gwarzon dan kwallon duniya din yaci kwallaye 202 cikin wasanni 286 daya bugawa Barcelona kuma sauran kwallaye 34 ya wuce Cesar Rodriguez wanda yaci kwallaye 235 a Barcelona daga shekarar 1942 zuwa 1955.