Capello ya sanya sunan Terry a tawagar Ingila

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kyaftin din Ingila, John Terry

Kocin Ingila, Fabio Capello ya bada tabbacin cewa ya sanya saunan kyaftin din tawagar Ingila John Terry a cikin 'yan wasan da za su taka leda da Spain da kuma Sweden.

A yanzu haka dai Hukumar 'yan sandan Ingila na binciken Terry bisa zargin yin kalamun wariyar launin fata ga dan wasan QPR, Anton Ferdinand.

Capello ya ce, ya yi magana da Terry a ranar juma'a kuma ya gana da wasu manyan jami'an hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Capello ya ce; "Na tattauna da suran jami'an kwallon Ingila kuma sun amince da in sanya sunan Terry a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su taka leda da Spain da kuma Sweden."

Ya ce tunda ba'a gama bincike ba, kuma ba'a same shi da laifi ba, dolene ya sanya sunan shi.