Gwarzon Afrika: 'Yan Ivory Coast uku sun samu shiga

Image caption Yaya Toure

Dan wasan Manchester City, Yaya Toure na cikin 'yan wasan Ivory Coast uku da su ka samu shiga jerin sunayen 'yan wasa 10 da za su yi takarar lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afrika na shekarar 2011.

Sauran 'yan wasan Ivory Coast din da suka samu shiga sune Didier Drogba na Kungiyar Chelsea da kuma Gervinho na kungiyar Arsenal.

Har ya wau akwai sunayen 'yan Ghana uku a cikin jerin 'yan wasan.

'Yan wasan su ne Asamoah Gyan na kungiyar Al Ain da Andre Ayew na kungiyar Marseille da kuma dan wasan AC Milan Kevin Prince-Boateng.

Sauran 'yan wasa da su ka samu shiga sun hada da dan kasar Morocco, Adel Tarrabt, da Moussa Sow na kasar Senegal sai kuma dan kasar Mali Seydou Keita.