Muhammed Ali ya jinjinawa margayi Joe Frazier

frazier Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Joe Frazier

Muhammad Ali ya jagoranci jinajinawa tsohon zakaran dambe a duniya Joe Frazier wanda ya mutu yana da shekaru 67 saboda cutar sakaran hanta.

Ali yace"duniya tayi asarar gwarzo".

Shima tsohon zakaran dambe Lennox Lewis ya ce "frazier gawurtaccen dan dambe ne a duniya".

Frazier ya lashe kyautar zinare a dambe na gasar Olympics a shekarar 1964 kuma ya zama zakaran duniya a shekarar 1970 bayan da aka kwace kambun a hannun Ali a shekarar 1967 saboda kin shiga yakin da Amurka tayi da kasar Vietnam.

Ali yayi kokarin kwace kambun amma sai Frazier ya doke shi a shekarar 1971.