Man City na saran dawowar Tevez a yau

tevze
Image caption Carlos Tevez

Manchester City na saran Carlos Tevez zai dawo horo a ranar Laraba, duk da cewar an ganshi ya isa Argentina a ranar Talata.

Dan wasan Argentina din ya tafi kasarsa ne a ranar da rahotanni suka ce ba zai kalubalanci tuhumar da ake masa akan takkadamar data taso a wasansu da Bayern Munich.

Kakakin dan kwallon Paul McCarthy ya shaidawa Sky Sports News cewar "ya tafi ya gana da iyalansa".

Tevez zai iya kara fuskantar ladabtarwa idan har akayi horo banda shi.

Yawancin 'yan kwallon Man City sun tafi hutu don bugawa kasashensu kwallo amma ya kamata shi ya cigaba da kasancewa a City don yayi horo.

Argentina bata gayyaci dan kwallon ba cikin tawagarta da zata fafata da Bolivia da kuma Colombia a mako mai zuwa.