Wasan Gabon da Brazil zai bude mana ido-Rohr

gabon Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Gabon

Kocin Gabon Gernot Rohr ya ce fafatawarsu da Brazil wani gwaji ne na musamman a yayinda kasar ke shiryawa gasar cin kofin Afrika na 2012.

Gabon na daukar bakuncin hadin gwiwa tare da Equatorial Guinea kuma a ranar Alhamis zasu kaddamarda sabon filin wasan kasar a Libreville.

Rohr yace"wannan wasan zai nuna cewar ko zamu iya fuskantar babbar tawaga".

Gabon na rukuni guda tare da Nijer da Morocco da Tunisia.

Wasansu da Brazil zai zamo manuniya ga kasarta ta Gabon.

A cewar kocin Gabon Gernot Rohr duk da cewar babu manyan 'yan wasan kamarsu Kaka da Marcelo a cikin, amma dai Brazil ba kanwar lasa bace.

Brazil ce zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014.