Neymar zai kasance a Santos har zuwa 2014

Kungiyar Santos ta Brazil ta sanarda cewar Neymar ya amince ya cigaba da taka leda a kulob din har zuwa shekara ta 2014 lokacin gasar cin kofin duniya da za ayi a kasar.

Shugaban Santos Luis Alvaro de Oliveira Ribeiro ya bayyanawa manema labarai cewar dan wasan ya amince ya sabunta kwangilarsa.

Real Madrid da Barcelona suna zawarcin matashin dan kwallon don ya koma taka leda a Turai.

Rahotanni sun nuna cewar a yanzu an yiwa Neymar karin albashi ta yadda zai iya karbar albashi irin yadda za a biyashi a manyan kulob a Turai.

Neymar yace" naji dadin wannan lamarin, na dauki hukunci ne tare da mahaifina da dan uwana".

Shugaban Santos Lius Ribeiro ya kara da cewar"mafarkinmu ya zama gaskiya kuma naji dadin ganin wannan ranar a rayuwata".