Euro 2012:Zan maida hankali akan matasa-Capello

capello
Image caption Fabio Capello

Fabio Capello ya ce matasan 'yan kwallon Ingila suna cikin shirinsa a gasar cin kofin Turai wato Euro 2012 bayanda 'yan wasansa suka doke zakarun kwallon duniya Spain daci daya me ban haushi.

Capello yace"matasan 'yan kwallon sun nuna kwazo kuma ina tunanin zasu je gasar kwallon Turai".

Dan wasanta Everton Jack Rodwell ya bugawa Ingila wasansa na farko a yayinda dan kwallon Manchester United Danny Welbeck shima ya nuna kwazo.

Haka zalika matashin dan kwallon United Jone mai shekaru 19 shima ya buga wasan.

Capello yace "naga yadda matasan yadda suka buga kwallon ba tare da tsoro ba".