Esperance ta lashe kofin zakarun Afrika

espence Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Esperance na murnar daga kofi

Kungiyar Esperance ta Tunisia ta lashe gasar zakarun kwallon Afrika bayan ta samu galaba akan Wydad Casablance ta Morocco daci daya me ban haushi a bugu na biyu a wasan karshe.

Dan Ghana Harrison Afful ne yaci kwallo daya a wasan da aka samu tashin hankali.

A bugun farko na wasan karshe a tashi babu ci ne.

Kenan Esperance zata wakilci Afrika a gasar kulob kulob ta duniya a Japan a wata mai zuwa, inda kungiyar data lashe gasar zata samu kyautar dala miliyon daya da rabi.

A lokacin wasan dai an kori dan wasan Wydad Mourad el Massane bayan daya kaiwa dan Esperence Yannick Ndjeng mummunar hari.