Redknapp zai fuskanci shari'a akan haraji

redknapp Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Harry Redknapp da Milan Mandaric

Kocin Tottenham Hotspur Harry Redknapp zai fuskanci kuliya akan zargin kin biyan haraji a lokacin yana manajan kungiyar Portsmouth.

Mr Redknapp da tsohon shugaban Portsmouth Milan Mandaric ana zarginsu da aikata laifuka biyu dake da nasaba da yin zanba akan kudin haraji.

Ana zargin cewar Mr Mandaric wanda shine shugaban Sheffield Wednesday a yanzu ya biya Mr Redknapp kudi kusan fan dubu 183.

A ranar 23 ga watan Junairun 2012 ake saran duk su biyun zasu gurfana gaban kotun Southwark Crown.

Ana saran za a shafe makwanni biyu ana shari'ar.

Mr Redknapp mai shekaru 64 yana zaune a Poole dake yankin Dorset kuma a kwananan aka yi mashi tiyata a zuciyarsa saboda toshewar wasu jijiyoyi.