Ina son Balotelli ya dawo Inter Milan-Moratti

balotelli
Image caption Mario Balotelli

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya ce zai so dan kwallon Manchester City Mario Balotelli ya kara komawa kulob din.

Balotelli ya bugawa Inter a kakar wasanni uku kafin ya koma City akan kusan fan miliyon 24 a shekara ta 2010.

Moratti yace " Zan so Balotelli ya koma gobe saboda yana burge ni".

Balotelli ya ciwa Italiya kwallonshi na farko a wasanda ta doke Poland daci biyu da nema.

Amma kuma Moratti ya kara da cewar baya dana sanin sayarda Balotelli.

Shima kocin Inter Claudio Ranieri yace "hannu na abude suke wajen karbar dan wasan".

Karin bayani