Tevez ya kara kauracewa horo a Man City

tevez
Image caption Carlos Tevez

Masu baiwa Carlos Tevez shawara shun bayyanawa BBC cewar dan wasan har yanzu yana Argentina a yayinda aka kara yin horo a Manchester City tare dashi.

Ba a gayyaci Tevez dob ya bugawa Argentina kwallo ba kuma City bata bashi damar tafiya ba, ya kama hanya ya tafi mahaifarsa.

City ta umurci lauyoyinta su dauki matakin daya dace akan kauracewar da Tevez yayi.

Amma dai masu bashi shawara sunce kawo yanzu ba a basu wani bayani ba akan batun ladabtarda dan wasan.

Karin bayani