Turkiya ta raba gari da Guus Hiddink

hiddink Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Guus Hiddink

Guus Hiddink ya sauka daga mukaminsa a matsayin kocin tawagar 'yan kwallon Turkiya bayan da kasar ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Turai da za ayi a badi.

Hukumar kwallon Turkiya ta ce sun cimma yarjejeniya tsakaninsu da tsohon kocin Chelsea don kawo karshen kwangilarsu dashi, duk da cewa kamata yayi ya bar kasar a shekara mai zuwa.

Turkiya dai tasha kashi daci uku da nema a bugu biyu na wasanni kifa daya kwala tsakaninsu da Croatia.

Hiddink mai shekaru 65 ya koma Turkiya ne a watan Agustan 2010.

A baya dai Hiddink ya jagoranci Netherlands da Koriya ta Kudu da Australia da kuma Rasha sannan kuma a bangaren kulob ya jagoranci PSV Eindhoven da Real Madrid da kuma Chelsea.

Kawo yanzu dai rahotanni sun nuna cewar kungiyar PSG ta Faransa da kuma Anzhi Makhachkala ta Rasha suna zawarcin Hiddink.